Hausa novels

SARKI SAMEER 1

littafin sarki sameer episode 1

💅SARKI SAMEER…. by ❤xeemat….love❤ 🌹🌹🌹Episode 1🖋🌹🌹🌹

Related Articles

Ina ma abota masoya makaranta littattafe kugarzayo nan domin kusamu naku rabon karku bari abaku labarin wannan litttafin me tafe da nasa sabon salon na daban wanda yasha bambam da sauran wanada ya hada da sarkakiya me wuyar fahimta da  tausayi😢makirci,mugunta😠san abun duniya,san zuciya,hassada babban ciwo gameyinta,bayan haka ba iya nan ya tsayaba ya hada da barkwanci da nishadantarwa da fadakantarwa  da kuma wannan babban abun me gabadaya watakon soyayya💞 hot romantic story💓ake gaya muku wanda babu kamarsa,
kude kubaza kunnuwanku da idanumku👀 domin ganin yanda wasan ze kaya gaba daya muje zuwa….

Ina fatan Allah yabani ikon farawa lfy da gamashi lfy batare da wata matsala ba  kuskuren da zanyi aciki Allah yayafe min, ina fatan zan samu hadin kanku baki daya Domin wannanne littafina na farko aduniya,Abun da yake me kyau mudauka muyi amfani dashi marar kyau kuma muyi watsi dashi.ALLAH YAKARAWA ANNABI DARAJA DA FADILA ALLAH YABARMU DA SONSA HAR ABADA ALLAH YAKASHEMU DA SON ANNABI MUHAMMADURRASULULLAH (S A W)

DAGA SABUWAR MARUBUCIYARKU ME SUNA AZEEMA D AMINU.(XEEMA…..)

BISMILLAH بسمللله

💅SARKI SAMEER💅 Episode one1
mom! mom!! mom!!! wata yar budurwa da baza ta wuce kimanin shekara 21zuwa 22 ba tashigo cikin falon ko sallama babu tana kiranta tana haurawa upstairs din dake falon after some mints ta sakko tana ta kumfar baki tana zagaya falon tana mamakin ina mom din nata tashiga bata gama tunaninba naga wata mata da bazata gaza shekara arba’in ba zuwa da biyu ko ma da biyar tana shigowa ta fadada fara’ar fuskarta tare da cewa a’a daughter yaushe kika shigo bata bata amsaba takaraso inda take tare da ruqo hannun ta tare dacewa mom wai kin san waccan yar iskar yarinyar can nagani tare da da BOSSAY sai wani faman washe mishi baki take harda kyalkyala dariya shikuma ya wani tsaya yakura mata ido kamar ze cinyeta ta karasa maganar kamar zata hadiyi zuciya ta mutu tsabar bakin cikin da take ciki mom din da tundazu ta zubawa diyar tata ido batace mata komai ba sai dan murmushi datake yi wanda bekai har zuciba tare da jan hannun ta zawa cikin falon ta zaunar da ita akan haddun kujerun falon da aka qawatasu da da abubuwan more rayuwa wanda tsayawa ma fadarsu bata lkcne kawaide kana gani kasan bana qananun mutane bane saboda ya hadu iya haduwa yaji dukiya acikinsa,ta dan shafa fuskarta batare da tace mata uffan ba ta wuce kitchen tadawo da tire a hannunta cike da fruit sai cop da lemo me sanyi  ta ajiye mata zatayi magana kenan yarinyar tai saurin katseta  cike da rashin tarbiya murya asama tace wai mom meye haka tun dazu ina tayi miki magana amma kinyi min banza ni banzan shaba ki dauke abunki banaso tafa tana qorin tashi tabar mata wajen.

cike da rarrashi tayi saurin maida ita tazaunar sannan ahankali tace haba my daughter ki kwantar da hankalinki akan dan wannan abun nibanga abun tashin hankaliba kwatakwata me akayi akai wannan kucakar yarinyar me kama da aljanun da marar asali marar gata watake da shi waye ubanta ita wacece ita dazatasaki kiringa wannan tada hankalin akanta haba haba kamar ba jinin cikas family ba kamar badaga cikikna kika fito ba tafada tana qara rike hannun sannan tace kibar min komai a hannu na zata shigo gidan tasameni zanyi maganinta ne daga ita har waccan tsohuwar banzar tafada tana kallon diyar tata   dataga alamun tadan saki fuskarta magangan  dani ba wlh takaicine yahanani yimusu magana ma danji nai kamar zuciyata zata buga idan nayi mgn shiyasa kawai na shigo gida in fadamiki karkada kai kawai tayi sannan tace gwara da kika rabu da ita kar kijama ta kara renaki agabanshi intashi za tamin bayani ne kisha wannan sannan kije kiyi wanka kishirya kifito  kiyi lunch kafin tashigo akentama fa nayi amma shine taje ta tsaya hmmm cike da jin dadi ta mike tanacewa mom bazan shaba bari kawai inje in watsa ruwa infito tafada tana barin wajen ta haura upstairs inda dakinta yake tana tafiya mom ma tatafi nata daki tana kara jaddada hukuncin dazatayiwa yarinyar nan idan tadawo suna shiga yarinyar data gamajin tattaunar tasu tashigo cikin falon tana rar raba ido  cike dafargabar abun dataji da tunanin kuma irin hukuncin daza ai mata yarinyace dabaza tawuce 14years zuwa 15 ba ita ba doguwaba ita ba gajeraba medium ce  duk da banga gashin kantaba amma nasan tanada gashi sosai saboda gashin danagani kwance a goshinta da ya kusan hadewa da gashin girarta ga wani uban saje da shima yake kwance luff luff awajensa ga uban eye lashes zarazara meyawa ga tsayi tana da manyan idanuwa farare tass da su kwollon idonta brown color idonta kuma sexy ne idan tana kallonka sai kadauka bacci ne a idonta fara tass kamar katabata jini ya fito amma saboda wahalhalun rayuwa ba aganin  hasken nata sosai sai dogon hancinta me tsinin gaske idan ka matso kusa da ita sai kai tunani inkamatso dab ze iya tsokanema ido sbd tsayinsa sai bakinta dan qarami kamar gidan tsutsa gashi pink kamar ta shafa abu akai  sai kirjinta da ya dan fito amma ba sosai ba sai bombom dinta da hips din dede jikinta basuyi mata yawa basuyi mata kadanba komai de yaji dede.

bata gama tunane tunanen ba taji anbuga mata wata uwar tsawa kwasa aguje zata fita taji ankara daka mata tsawa tare da cewa gidan ubanki zaki dan uwarki idan kikasake kibar falon nan sade uwarki ta haifi wata a lahira idan ana haihuwa kokuma waccan banzar tsohuwar ta haifi wata irinki idan zata iya shegiya me kama da aljanun da ido kamar na mayya waya sanin ko mayya ce bamu saniba cikin dacin abun da tafada mata ta juyo a hankali kamar wacce ba qashi ajinkinta yayin da waye suke zubowa kamar ruwan sama suna wanke mata fuska tana qarasowa bata ankaraba taji anyi mata wawuyar shaqa tare da ruqe kunnanta kamar za acire mata shi da sauri tasa hannunta zata dafe wajen taji anriqe mata hannun tare da murdeshi tabaya cike da mugunta abun ya hadar mata ga wuyanta ashaqe ga kuma kunne a murde tanaso tayi magana amma takasa saboda shakar da akai mata ba qarama bace tana kakari amma ta kasa furta ko kalma daya sai da kyar tasamu ta sassauta mata ruqon wuyan cike da tashin hankali ta da muryarta da dashe tace Dan Allah mom kiyi hakur…bata qarasa bada hakurin ba tace dan ubanki ban hanaki kirana da mom ba uwarkice ni dazaki kirani mom ko ban hanaki ba dasauri ta shiga girgiza kai tana cewa kinhanani kiyi hakuri bazan qaraba na tuba tace kima sake tafada tare da cewa daughter saketa kibarni da ita nika daima na isheta cike da jin dadi ta sakar mata hannun tana cewa yauwa mom kar kiraga mata wlh ita kuma kamar akeyiwa kirari haka ta daddage da iya qarfinta da Allah yabata ta kifa mata marin da saida taga ster kafin tagama tantance zafin takaraji wasu marukan da saida tasaki wata razanarniyar qarar da ta karade duka gidan tanasakin qarar kuma ta sume agurin mom naganin haka ta tabe baki tanufi wajen fridge ta dakko ruwa me sanyi ta watsamata agigice kuwa ta tashi zaune tana jada baya tana hada hannuwanta da suke tafaman karkarwa tana kara basu hakuri amma basu saurareta ba kuma ko kadan basu tausaya mata ba sai qara dagata da tayi da gashin kanta tana janta har zuwa kaofar kitchen tana fadar yau saina yanka ki inga uban da ya tsaya miki kikeyiwa mutane rashin mutuncin dakaga dama acikin gidan bata qarasa shigaba.

wani saurayi yayi saurin qarasowa gurin yana riqe hannunta da fadin haba mom mekike kokarin yine haka tundaga waje akejiyo ihunki duk akan wannan yarinyar me tayine cike da masifa tadago tana cewa MUSBAHU sakar min hannu kafin indawo kanka ni kacewa ina Ihu ko gani mahaukaciya tafada tana fisge hannun ta zata qara kamo ta yayi saurin tsayawa atsakiyarsu yana cewa dan Allah mom ki tsaya  kisaurar.. be karasaba tace anqi a saurare kadin ubana kamatsa min daganan ko sainayi maganin ka ai yau sainaga uban da yatsaya mata agarin nan be ankara ba tayi wani tsalle ta kamota ta rike gam tajuya in yar tata take tana tafaman rarraba ido tawani gurin tajin haushin zuwa dayayi zesa aqi hukunta yarinyar kamar yanda takeso tawani gurin kuma tana jin zafi saboda tsoran yayan nasu tace daughter zo kiwuce ki dauko min wuqa a kitchen tafada tana qara riqeta da kyau saboda musbahu da ya riqeta shima yanso yajanyeta daga hannunta tazo zata wuce kenan yada ka mata tsawa tareda cewa wlh RASHEEDA indan kika dakko ke zan yanka da ita aikwa nan da nan tatsaya cak tana tunanin umarnin waza tabi…………
+
anan na kawo qarshen p1 sai mun hadu a na2 muje ya wasan ze kare RASHEEDA zata daukko ko bazata dakko ba
muje zuwa daga sabuwar marubuciyarku

❤xeemat…love❤

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

AdBlock Detected

turn off ad blocker to access this site