
💅SARKI SAMEER…. by ❤xeemat….love❤ 🌹🌹🌹Episode 5&6🖋🌹🌹🌹
cigan labari*
Furgigit dadda tayi tadawo daga duniyar tunanin da ta tafi sakamakon tabatan da Ameesha tayi ajiyar zuciya tasauke tare dacemata wai harkin gama shiryawar eh tace mata sannan tace nadadema dashirya wa harmafa naci abincin kuma tundazu nake miki magana amma kintafi tuna nin dakika saba waima dan Allah dadda kigagaya min abun da kike tunani kullum baki da aikin yi sai tunani ahankali tace hmmm bazaki gane bane Ameesha amma kiqara hakuri akwai lokacin dazan gaya miki komai sai kin kaqara girma tukunna baki Ameesha ta turo mata baki tace daman ai kullum haka kike cewa dadda ni wai duk wannan girman danayi wane irin girma kikeso inyi kuma tace saikin qara hankali tukun tace kina nufin daman kallon mahaukaciya kike min da sauri tace mata a’a nibaceba daga cewa sai kin kara hankali sai kuma kimin sharri ni yaushe kikaji nace miki mahaukaciya to dadda mekike nufi dahakan duk wanda akace mishi sai yayi hankali ai ana nufin mahaukacine shi tace to yi hakuri ni bahaka nake nufiba kizo kitafi kawai tunda naga bakida niyar baccin naga alamun yay ‘yan tsiwarne suka motsa dan qara min bakinta taqara tura mata batace mata komai ba ta juya zata fita cike da jin haushin zantukan daddar tata ta tsani taga tana wannan tunanin da itabata san amfanin shi ba(nace injikiba)tana jiyo maganarta tanacewa au ko sallamama bazaki min ba to sai kin dawo Allah yakiyaye hanya kinji ko kigaishe min da maman Azeeman.
ko tsayawa bataiba bare tasa ran zata amsa mata ahaka tai ficewarta amma ta amsa mata da ameen acikin zuciyarta tana fita dadda tace ja’rar yarinya kawai me tsiwar tsiya da bata da gurin yinta sai akaina dake ni ta raina ai kin iya zuwa ana da miki na jaki bazaki tabuka uban komai saide ni kidawo gida kina min kuka kuma inrashin mutunciki yatashi ki saukeshi kaina ni ban ma san ubanwa kika dauko wannan halin ba dan nasan duk iskancin gyatumarki batai irin wannan ba ita kadai sai faman zuba take dadda bade mita ba….
Ameesha nafita direct gidan su Azeemar ta nufa tana zuwa ta bubuga gidan wani saurayi yazo ze bude sai kuma yatsaya yana cewa waye tace ya SALEEM nice kantagama fadama ya bude da sauri yana sakin qayataccen murmushi yace A’a ashe babbar bakuwa mukai barkanki da zuwa itama da fuskarta dauke da murmushi tace yauwa ya saleem barkan kade nasameku lfy yace lfy lau wlh shigo daga ciki mana kintsaya awaje sai kace gidan bakonki ne yafada yana matsa mata tashige ciki tana murmushi shikuma yarufe gidan yabiyo bayanta suka shiga cikin falon tare yazauna sannan yace mata kishiga ciki maman bata nan amma azeemar tana ciki kije inkun gaisa kuma kizo muyi zance anan ina jiranki tace to ya Saleem bari inshiga infito shima yace mata to amma dan Allah karkidade idan kuma kika dade harciki zanshigo in dakko ki wlh dariya tayi tace kar kadamu hakanma baza ta faruba yace tama farudin kiga aiki da cikawa yarinya yafada yana dan mata hararar wasa bata cemishi komai tasan inta biye mishi ba barinta zeyi ta wuce ba dariya kawai tayi tashige ciki shikuma ya kwantar da kansa y naana wani lumshe idanu yanajinta harcikin ransa yake jin sanyi idan yaganta tana shiga ta tarar da ita tayi dai dai tana sharar bacci hankalita kwance qarasawa tayi gaban gadon nata tanacewa yarinyar nan bata gajiya da bacci wlh kullum mutum sai kace me cutar sleeping skilles hannu tadaga sama da iya qarfinta da Allah yabata ta dala mata duka a bom bom dinta.
aikwa amatuqar fugice ta tashi tana niyar kwasa aguje tabar dakin dan zafin dataji yasa tama manta a ina take dariyar muguntar da Ameesha take tafamayi ne ganin yanda duk tabi ta furgita daga dan wannan dukan datai mata aikwa a hassale tatsaya tana kallon ta tare dakai mata duka tana fadin wlh sai Allah yasa kamin idan banyafe miki ba wannan ai cin zaline da mugunta kinsan yanda kika tsoratani kuwa ina cikin bacci na me dadi kizo kitasheni kuma ma da irin wannan dukan haka takarasa maganar kamar zatafashe da kuka saboda takaicin abun da qawar tata tai mata cikin kunshe dariyar ta da take cinta tace ayya besty ta takaina besty ta nikadai I’m so sorry kinji nibansan zaki tsorata har haka ba kinji qawalli ta harara ta watsa mata tace anqi hakurin kitaahi ki koma inda kika fito ni ba ruwana dake ko a hanya kika gani kar kinuna kinsani yar rainin hankali kawai da wani bakinki tunna haihuwa da be qara girmaba kina min dadin baki to bazan hakura din ba taqarasa fada tana mikewa zata barmata dakin tiyi saurin tare gabanta tanacewa haba dan Allah nafa baki hakiri plssssss mana natuba bazan qaraba ta riqe kunnata tana matrairai cewa kamar zatai kuka sai lokacin bestyn tata tadan saki fuska tace naji to tace kin hakura kai ta daga mata alamun eh aikwa da sauri ta rungumeta tanacewa yauwa besty nagode.
daman nasan fushin ba inda zashi nasan dole zaki hakura qoqarin tureta tayi tana fadin au dole ma kikace ko da sauri tace aa wlh da wasa nake tace hmm da bansan halinki bane sai inyarda taraba jikin ta danata sannan suka koma suka zauna Ameesha ta oh ni yar jikar mutum daya nataho da murna ta dannazo na ganki amma nazo sai wani faman wulakanta ni kike tace kikade wulakanta kanki da baki min mugunta ba ai da duk haka bata faruba tace to nide abar maganar komai ya wuce naji zuwa nai kiban shawara akan gidan aikincan danakeyi wlh nagaji da cin mutuncin dasuke min kullum wahalar yau daban ta gobe daban ta gobe daban kullum acikin cin zalina suke dayi min mugunta iri iri kinsan dazu Allah ne ya taimake ni amma da tuni yanzu ina barzahu shegiyar matar nan da jikinta kamar na buhun dankali takusa yimin yankan da akeyiwa rago tsabar rashin imani Azeema ce ta katseta da cewa nashiga uku ni Azeema wane zunubin kika aikata mata haka tace hmm wlh kawai muguntace da baqin hali irin tasu ita da yarta amma ni banga abun laifi anan ba wai kawai dan BOSSAY yazo nikuma nazo fita an aikini sai yakini naje muna gaisawa…….nan de ta kwashe duk abun da yafaru atsakaninsu da kuma abun da sukayi mata ta fada mata tana qara jin zafin abun aranta tana dan goge kwallar da ta zubo mata hannuwanta ta ruqe.
tace Allah sarki besty kiyi hakuri dan Allah gaskiya na tausaya miki kuma ai Allah ba azzalumin bawa bane yanasane dake kuma zebi miki hakkinki nacin zalin dasuke miki Allah yasakamiki tace Ameen tace ni wlh daman dazaki bi tatawa dakin dena zuwa ma gaba daya tace nima ina tuna nin hakan to amma kinsan kudin da sukeban dashi nake samu inyi duk wani abu daya kama inyi amakaranta dasu nake biyan school peas dina idan nadena zuwa waze nabiya mun wadannan abubuwan kinga dadda bawani kudi ne da itaba itama kudin datake aiki dasu muke dan samu muna cin abinci da kuma dan qananu abubuwa da baza arasaba wlh bansan ya zanyi ba amma harga Allah nagaji da rayuwar nan da muke ciki tafada tana qara goge hawa yanta da yake zubowa cike da damuwa da tausayin qawar tata tace hakane kuma kiyi hakuri kicigaba da kai kukan ki gurin Allah in sha Allah nasan wataran zakiji dadi arayuwar ki Allah ze share miki kukanki yana sane dake nide shawarar da zanbaki kawai kicigaba da hakuri dasu goben kawai kishirya kije gidan sannan kibata hakuri ko me zasuce miki kar kida kai ki kallesu kuma kar kisa komai aranki tunda de kin riga kinsan halinsu kidena bari magan ganinsu suna tasiri akanki kibarsu da Allah kawai shize rama miki tace to ni wlh tsoro nake ji karnaje ko sunshiryan wani abun ina zuwa sukasheni ko suban guba inmutu tunda ba qaunata suke ba kuma basu da imani ko kadan.
tace karkiji komai wlh in Allah ya yardama ba abun dasu miki ai Allah yafisu kawaide ki dage da addu’a Allah ya tsallalar dake daga sharrinsu tace ameen zan gwada zuwa goben Amma nasan da kyar inbazasu qara yimun wani abun ba tunda bahaka suka soba ya musbahu yazo ya tamakeni tace kede wai banace kidena damuwaba kawai ki kwantar da hankalinki tace to shikenan nagode da shawarar ki bari inzo in tafi gida kar magrib tamin tafada tana miqewa tace to muje in dan taka miki kinga kuma mama bata dawo ba har zaki tafi tace kar kidamu ai watakil ma zuwa jibi inqara shigowa tunda ke baki da mutun ci bazuwa inda nake kike ba tace kinsan halin mama ai ba kullum take barina fita ba hmm kawai tace sannan suka fito daga dakin suna fitowa idonta ya sauka akan saleem da yake ta faman zabga mata harara tai saurin cewa laa ya saleem dan Allah kayi hakuri wlh namanta shaf na sha’afa muna ta hira yace daman mana kinshayani tun dazu ina tafaman jiranki ko kin kyauta nagode da wulakanci daman ai kinsaba tace tuba nake yayanmu aimin afuwa bani qarawa saiki gayawa wanda besanki ba komai kikai saiki wani ce ayi hakuri bani qarawa amin afuwa kuma ko goben sai kin qara yafa da da kwaikwayan muryata yanda take dukansu sai suka sa dariya saboda yanda yanayin maganar yace shikenan saiki tafi daman haka kikeso ba kyaso kizauna muyi hira yana fada yamike ya wuce dakinsa tace babban yaya ayi hakuri be tanka mataba yayi wucewarsa ita kuma tace uhm besty mutafi ina kara dadewa tace to muje suka fito suna tafiya suna yar hirarsu har takawo ta dede wata kwana da tanabi zata kai hargida sannan sukai sallama kowacce tatafi gidansu……
Musbahu be dawo gidan ba sai bayan sallar isha’i yana dawo wa kwa be tsaya ko ina dan baya son haduwa da mom dinshi ya nufi part dinshi saidai kuma kashh bekai da shiga ciki ba ya tsinkayo muryarta tana cewa to munafuki ina zaka ai daman ai daman zaman jiranka nake zaka wani zo kawuce sumsum kamar barainiyar mage dawo wa yayi yazo har inda take atsaye yace mom bafa abun dakike tunani bane ni bawai wucewa naiba inasane kawai danna ga bakowane shiyasa na wuce tace karya kake kuma gidan ubanwa kakai ta yace mom gidansu nakai ta mana dan Allah mom kidena irin wadannan abubuwan kina batawa kanki lokaci akan ‘yar shilar nan dabata da komai bata dakowa ni wlh mamaki ma nake idan naga kina daga murya akanta shiru tayi tana sauraronsa sannan yaci gaba da cewa ni yanzu abun danake so dake kirabu da ita ni da kaina zanyi miki maganinta da kaina basai kin wahalar da kankiba ai kinfi qarfi kiringa tsayawa da ita wataran ma ai sai ta rainaki kawai kirabu da ita kibar komai ahannu na zakiga yanda zanyi da ita yanzuma da na fita da ita ai bakiga yanda naimata naci mutuncin ta akan wahalar min ke da tayi ko da wasa gobe bazata sake aikata kwatan kwacin abun da tayi yau ba ajiyar zuciya ta sauke sannan tafara washe baki dajin batun dan nata harda rungume shi dan jin dadin kalamansa sai yanzu tagane ashema zubar da ajinta takeyi akanta taba kin nashi kuma da gaskiyar shi tasan idan taci gaba watarana yarinyar nan sai ta mayar mata da martani dan ta lura da ita kamar zatai tsiwa watakil tana raga musune dan sunfi qarfinta kuma tana aiki aqar qashinsu ne shiyasa amma idan suka qureta wataran reshene zai juye da mujiya sunanta da yakirane yadawo da ita daga tuna nin data tafi ta amsa masa da yauwa son wlh harkasa naji sanyi araina wlh ai na dauka bayanta kakebi shiyasa kaji ina tai maka haka amma yanzu tunda ka ganar dani kuma ka dorani ahanya daga yanzu ba abun daze kara hadani da ita bare hartakai da renani zan ringa hade mata rai ba ruwana da ita idan kuma tai min kuskure duk min qanqantarsa zan gayamaka ka hukunta min ita.
yace yauwa mom haka nake son ji dazarar ta miki ba dede ba ki gaggauta sanar dani kawai tace to shikenan ba matsala wlh baka ji yanda naji dadin maganar nan taka ba yace mom ni bari inshiga ciki dan wlh agajiye nake tace to baka ci komai ba haka zaka kwanta yace kar kidamu naci abinci agidan su wani abokina tace to shikenan sai da safe yace Allah yakaimu sannan ya wuce yana cin dariyar mahaifiyar tashi da tayarda da shirgatan dayayi ta yarda kuma lokaci guda bahama giya kawai(inji ni fa ba injishiba)yana tafiya itama ranta fes fess tahaura sama kai tsaye bedroom din Rasheeda ta nufa tana shiga tasameta tafito daga wanka tana shafa mai taje ta zauna abakin gadon nata tana kallon yarta ta tace my daughter you know what?tace no mom saikin fada naga tunda kika shigo kike sakin smiling what happened tace hmm ashe duk shirme muke akan yarinyar nan sai yanzu da yaron nan yake ganar dani sannan nagane duk yanda sukai da shi ta kwashe taga ya mata tana taqara sakin smiling taga yar tata ko juyowa ma basai ba bare ta tanka mata tace daughter yade naji kinyi shiru bakice komai ba ko bakiji dadin hakan ba shiru tayi mata ba amsa tana tunanin yama za ai hakan tafaru yaya musbahun da ko laifi kaimishi befiya daukan matakiba har saika kureshi sannan zakaga bacin ransa da irin matakin daze dauka shine kuma har ze gaya mata wannan maganar tayarda da wannan ta tsuniyar tashi dan wlh wannan tatsuniyace kawai ba wani mataki da ze iya dauka amma tunda ita mahaifiyar tata bata gane ba gwara kawai ta rabu da ita idan taga beyi komai ba dakanta zatagane cewa shirgata kawai yayi dan haka kawai sai tajuya tace wa mom din tata sannan tace mom hakan ma yayi kawai kibarshi da itan tunda haka yabukata tafada mata tare da kakalo murmushin da bekai zuciba iyakarsa kan lebe itama murmushin takara yimata tare da cewa niko ina sakon da nace miki kije gurin saratu kikarbo min tashi tayi daga inda take tana tafam yatsina fuska tace ni wlh namanta sede gobe idan ban mantaba naje inkarbo miki tace to shikenan ai sai goben kawai tace uhm hum tana qarasawa wajen makekiyar wardrobe dinta tazuge part of dressing sleep ta dakko wata fingileliyar riga iyakar ta gwaiwa amma tana da dan kauri kadan tasaka tadawo wajen bed dinta da har yanzu mom din tata tanazaune agun tana kallon saida tahau kai sannan tace mom why are you looking at me like dat ta dan girgiza mata kai tare da cewa nothing tace ok am sleep so u can leave tace to shikenan good night tafada tanaqarasa fita daga dakin ita kuma taja blanket takwanta ta kashi light din dakin ta dauko wayar ta tashiga contact dina ta dannawa wata number call da naga anyi saving dinta da my everything tana kira har tagama ring ba adaga ba har dada takira wajen sau goma amma no answer haka ta hakura tayi cilli da wayar gefe tanjin haushin kin dagawar da yayi haka ta kwanta sai faman juye juye take takasa baccin tana cikin hakan taji wayar tafar vibrantion da sauri ta dauka tana yin answering gudun kar kiran ya katse(nace badan jan aji irin namu na mata kar kibada muman malama Rasheeda)
tana daga daga can bangaren Akace assalamu alaikum babyna ahankali ta lumshe idonta tanajin yanda sonshi ke qara shigarta ko sallamar da yayi mata bata amsaba tace cike da shagwaba tace babyyyyy harda wani jansa u don’t pick my call why yace am sorry wlh bana kusane kuma bagashi nakiraba kinsande inagani bazan qi daga warkiba ko dan turo baki tayi kamar tana gabansa tace to naji ykk yace lfy lau and you tace ba lfy ba yace what wrong with you baby na fada mun tace duk bakai bane yace nikuma me nayi tace dazu bana ganga da wannan banzar yarinyar ba kuna tafam dariya kuma sai kallon ta kake tayi tafada kamar zatai mishi kuka budar bakinshi sai cewa yayi which girl kike magana cike da takaicin tambayar tashi tace kana nufin baka santa ba shikuma yanasane yace mata haka saboda banzar data kira da yarinyar shiyasa yace mata be gane wacce take nufiba sannan yace nifa kin min bayani yanda zan gane kwata kwata ban fahimci wace banzar yarinyar kike nufi ba a hassale tace mishi yar aikin gidan mufa nake nufi yace ohhh wai baby meesha kike nufi ai sai yanzu nagane ni nama manta munhadu yau daman nazo ne zan…..bekarasa zance da yake yiba da qarfi tace what… menaji ka kirata dashi shiko saida yajanye wayar da ga kusa dashi yagama dariyarsa ganin yanda tai magana da qarfi kuma daman dagan gan yai hakan yasan hakan zata faru dan yasan kwata kwata bata son yarinyar shiyasa yayi mata haka yana gamawa ya mayar da wayar kunne yace hello hello baby wai mekike cewa bafa najinki tace nima ai banjika dazu amma yanzu inajinka yace nima haka watakil network ne yadauke shiyasa tace eh haka nace me naji kakira sunan yarinyar nan dashi dazu yace baby meesha yakara fada mata batare dajin komai ba tace mekake nufi kenan yace da ranki yagaya miki tace au haka ma zakace yace to da mekikeso ingaya miki nifa wlh bana son wannan qorafe qorafen naki ke kullum baza ai hirar arziki da keba sai kin ce ke kaza ke kaza bana miki kaza wace uwa wace arziki wlh nagaji dajinsu yakamata ki nutsu kasan inda yake miki ciwo da bazan juri irin wadannan abubuwan nakiba yana cikin magana kawai yaji tasakar mishi kuka aikwa atake yayi tsaki kawai ya kashe wayarsa tanajin hakan takara fashewa da wani kukan me cin rai tana ayyana abun da zatayiwa yarinyar nan dan aganinta duk ita taja mata yazo yana yimata wannan fadan ahak taci kukanta ta gaji tayi shiru ta qara saqe saqen abubuwan zata yi gobe ahaka har bacci barawo yazo yadauke ta……….
**
daga sabuwar marubuciyarku🖋
❤xeemat….love❤
Don’t forget Pls comment and share it