Hausa novels

SARKI SAMEER 3&4

cigaban littafin sarki sameer kashi na 3&4

💅SARKI SAMEER…. by ❤xeemat….love❤ 🌹🌹🌹Episode 3&4🖋🌹🌹🌹

Related Articles


        WACECE DADDA?

                BAGWADAS
DADDA tsohuwa ce me dattako da taka tsantsan akan abun dazesa mutuncinta yazube awajen mutum tana da hakuri da kawaice ba tashiga abun da be shafeta sannan kuma bata son raini ko kadan yar asalin garin bagwadas ce wani yankine agarin DAMATURU  Asalin sunanta kuma KHADIJA wanda wasu mutanan suka fi kiranta da hadizatu yar farace ba laifi tana da kyau dede misali kallo daya  bazaka ce mata muguwar kyakkyawa ba sai ka kalleta sosai zakagane silent beauty ne da ita kuma tana da dan jiki amma ba sosai ba (bata kai hajiya Halima shirgegiya ba😅😅) itakadai ce awajen iyayenta basu da kudi amma basa rasa abun dazasuci suna da dan rufin  asiri tunda baza ka kirasu da talakawa tukuf ba mahaifiyarta ta rasu tunda dadewa dan haka ahannun kishiyar maman ta taso tasha azaba kala kala agurin ta saboda bata taba haihuwa ba dalilin dayasa kenan da batasan darajar ‘ya’ya ba tsaya bada labarin rayuwarta bata lokacine muyi gaba kawai ma gane anan gaba tana cikin wannan  halin yau dadi gobe wuya duk dadema wuyar tafi dadin yawa Allah yataimaketa yafito mata miji da fitowarsa dayin auren ko wata daya ba a rufa ba babanta yabashi aurenta Mlm ISYAKU me gwanjo sunan mutumin da ta aura kenan shima acikin garin yake yanada rufin asirinshi daidai gwargwadon samunshi bayan bikin su da sati biyu suka bar garin yadawo da ita GOMBE suna zaman lafiyarsu ba wanda yakejin kansu tunbata sonshi hartafara saboda irin kulawar datake samu awajensa cike da so da kauna suke rayuwarsu saidai haryanzu Allah be basu haihuwa  ba abun kullum yana damunta tana tunanin ma anaya zata taba ganin jinita tana ganin kamar bazata taba haihuwa ba ita de tana son yara kodan suzame mata abun kallo nan gaba tunda bata da kowa ayanzu sai mijin ta tajiyo sallamar me gidan nata ita takatse mata tuna ninta daga inda take tasa ka buta agaba tana kalla dasauri ta mike tana fadin sannu da zuw…bata qarasaba maganar ta makale tare dawani zaro ido waje kamar zasu fado ganin yanda tatsorata yasashi qarasowa gurin da take aikwa da sauri taja baya tana fadin mlm me kake qoqarin yine sai kace makaho dan aljanune fa kaje kadauko mana wlh kafita dashi dakar kajamana masifa da bala’i muna zaman zamammu wlh bada niba.

tana kaiwa nan tai kokarin barin wajen yayi saurin ruqo hannuta yafara janta zuwa falon tanajanye da fadin nifa wlh kasakar min hannu na yace wai dan Allah hadizatu meye hakan kikeyi sai kace qaramar yarinya ki nutsu mana ki sairareni sai lokacin tai shiru tashiga binshi kamar yanda ya bukata din yanashiga falon ya ajiyeta akan kujera sannan yace ni wlh kinban mamaki ma yaza ai ki ringa dan gantashi da aljani mutum nefa kamar ke, ke dazakidazaki murna ma da ganinshi amma sai kihau surutai yo ni mlm badole ince aljani ba wannan kyan nashi ai bekama da na bil adama tafa da tana kara kallon yaron sosai tana kallon qafarsa taga ba kofoto  wai duk dan taqara tabbatarwa mutum ne  ajiyar zuciya tasauke tace to mlm gayamin inda kasamoshi yaron yakalla sannan yace yaron kirki jeka gurin ummanka kaji yaron da yake kallon cike da rashin sani da kuma rashin sanin abun dasuke cewa ahankali yataka zuwa inda take da sauri tarike shi tana rumgumeshi tsam ajikinta kamar zata meda shi cikinta saida tagama sannan ta dago shi tanace wa small boy what is your name kawai saitaji yace mata sunana SAMEER da mamaki ta juya tana kallon mlm dashima su yazuba wa odo yana tuna nin dama danshine yanda ta ruqeshi abun sha’awa kamar danta yana cikin tunanin yaji tace laa mlm kaji ya iya hausa da wlh har ina tunanin yanda zanmishi magana tunda nide ba wani iya turanci naiba sosai  bare in mishi ashema duk mune shima dariya yayi yace nima ai nazata ma baya magana ko kuma bayajin hausa tunda nataho dashi nake tai mishi magana amma ba uhm bare um um har muka qaraso nan tace tab dijam yauwa tsayama fara gaya min inda ka dakko shi tukunna saida ya gyara zama sannan yace wlh ina kan hanyar da wowa awajen umguwa sarire naga mutane da yawa sun zagaye gurin to kinsannide banason inga ana rigima.

kawai sai naje na kutsa kai nashi ina shiga kuma naga yaron nan akan wata baiwar Allah da take akwance ga jini sai zuba yake daga kanta yana ta faman kuka yana cewa ummi ummi amma ko motsi batayi kamarma marar rai dasauri naqarasa gurin nakamo hannun shi sai yayi sauri yana faman rirriqeni yana tuna min inda take sai na rungumeshi najuyo ina cewa mutanan yanzu Dan Allah saikace ba musulmai ba kuna ganin halin da take ciki ita yaron ta amma ba Wanda zai taimakesu kun tsaya kun zuba musu ido haba dan Allah ina gama fadar haka wani Alhaji yakaraso inda nake ya miko min hannu muka gaisa sannan yafara min bayanin cewa yakira motar asibiti yanzu zasuka raso yaron kuma dayagani bawanda beje wajensa ya rarrashe shi ba amma yaki yarda da kowa shiyasa kawai suka zuba musu ido amma ba dagan gan hakan tafaruba sai lokacin nadanji hankali na ya kwanta kuma alamu sun nuna cewa cewa shi yabuge matar kenan suna cikin haka motar asibitin ta karaso dasauri suka karaso suka sata a motar sannan alhajin yace suyi gaba gashinan zuwa sannan suka tafi sai yajuyo yakallani yace to alaramma yaron fa zamu tafi dashi nace to na miqa mishi yaron amma sai yaqi yarda fur yaje gurinshi shi dole sai ni da naga haka sai nace alhaji meze hana kabarmun shi awajena inyaso sai in baka number ta duk yanda ake ciki sai kagaya min idan tasamu lfi koma rasuwa tai duk da dema bama fatan hakan Allah yaba ta lfy de shine fatan mu.

yace Ameen sannan yazaro waryasa a aljihu yace infado mishi ta karanto mishi ya rubuta sannan yace to shikenan ni zanwuce duk yanda ake ciki zakajini sai musan abun yi kuma daga ita har dan nata sabo da natambayi ina danginta suke wani yace min wlh bawanda yasan daga ina take kawai suma wayar gari sukai suka ganta agurin ita ba me hankali ba kuma bazakace mata mahaukaciya ba tunda kayan jikin tsaf tsaf complete amma  kuma tambayar duniya anmata amma ko saudaya bata taba bude bakiba bare musa ran zata amsa Saide duk wanda yaji tausayinta yabata abinci takarba tabawa yaronta yaci yakoshi sannan taci sauran kuma kullum tana rungume da danta bata sakin shi ko kadan bare ataimake shi ahak take rayuwa har zuwa yau da ban kula da itaba na bigeta wlh kwatakwat ban lura da tahowar taba yakarasa gaya min cikin sanyin murya sannan nace Allah sarki haka Allah yatsara yaje kawai Allah kiyaye gaba yace Ameen sannan yashige motarshi yakara gaba nikuma nadora yaron amashin muka taho kinji yanda akai ni sai yanzu ma nake jin takaicin nima da na amshi numbarsa da yanzu sai inkira inji yanda akeciki nauyar yiyar ajiyar zuciya ta sauke cike da jimamin labarin da yabata tace gaskiya de Amma ai yace ze kiraka kuma nasan ze kira din tunda yafa da mujira zuwa gobe mugani yace to Allah yakaimu goben ta amsa masa da Ameen   sannan ta maida kallon ta ga yaron da yadade dayin baccin wahala ya lafe ajinkinta sai faman ajiyar zuciya da yake saukewa  tashafa fuskarshi cike da tausayinshi tace Allah sarki Allah yabawa mahaifiyarka lfy Allah yaraya mana kai ya amsa mata da Ameen yana mike wa daga wajen yana fadin ni bari inje in dan watsa ruwa in fito kafin yatashi inje in in dan siyo masa kayan sawa da abubuwan yara yadan rage zafi  ki kula dashi yakarasa fada yana shigewa daki da to amsa mishi sannan  itama tamike daga gurin takai shi dakinta takwantar da shi tundaga wannan rana ba labarin Alhaji shiru shiru tun suna jiran tsammani har sukacire rai baki daya suka cigaba da kula dashi tamkar dan cikinsu haka suke bashi kulawa har yagirma dan shi kanshi zuwa yanzu ba abun da yake iya tunawa arayuwarsa ta baya suma kuma basu taba nuna mishi basu suka haifeshi ba  saboda lokacin da abun yafaru bashi da wayo befi irin shekara uku ba inma yakai dan haka ba abun da yake tunawa dan zuwa yanzuma har sun sakashi a makaranta tun yana yaro yan mata suke rububi akansa.

ahaka ma wai begama girmaba yazama saurayi lokacin suna qoqarin fara jarrabawar Junior waec yayin kuma da shekarunsa yakai 15 kwatsam sai ga ciki ajikin hadizatu sunyi farin ciki sosai da samun wannan ciki  murna ba a magana tsakanin waddanan mata da mijin sunci gaba da ta rairayar cikin a haka har watannin haihuwata yayi ta suntulo yarta kyakkyawa tubarukallahu Masha Allah haka ranar suna yarinya taci suna NADEEYA ahaka suka cigaba da rainon ta suda da sameer dan shi kamarma yafisu sonta kullum tana hannun sa abun biyune yake rabashi da ita bacci ko idan yatafi makaranta yana dawowa lwa za kara daukata itama kuma tasaba da shi dan ko kuka take tana ganinshi zata fara wangale baki tana dariya ahaka suke rayuwarsu cike da farin ciki hartayi wayo sosai kuma wai duk wannan tsawon lokacin da suka dauka dadda ko saudaya bata taba marmarin zuwa gidaba saide shi wani lokacin yana zuwa yaga yan uwansa yadawo yayi yayi da ita suje amma tace ba inda zata saboda tasan inma taje ba dadi zataji ba kuma bata da kowa sai mahaifinta shikuma kishiyar mamanta ta mallakeshi ko takanta bayayi bare har yasaurareta kwatakwata baruwansa da ita shiyasa itama bata damu da ganin nasaba saboda tana ganin kamar da saninsa yakeyi mata haka har nadiya takai wajen shekara goma bata jeba saida akace mahaifin nata ba lfy sannan suka shirya gaba daya suka tafi tun ahanya take jin gabanta na faduwa.

suna zuwa tundaga qofar gidan taga mutane jikin ta yabata ko ba agaya mata tasan shikenan ta rasa mahaifin ta bata lokacin da hawaye suka shiga rigerigen sakko mata akan fuskarta sai yanzu take nadama da dana sanin abun datayiwa mahaifinta tasan bata kyauta ba duk lalacewar uba ubane ba acanza mishi suna da wannan tunanin taqarasa shiga cikin gidan ita da nadeeya shikuma mlm sun tsaya awaje shida sameer suna gaisawa da mutane tana shiga wata qawarta tun lokacin da take garin tazo ta rungumeta da yimata ya hakuri haka de akai ta jajantawa juna bata tafi ba kwa saida tabari akai sadakar bakwai saboda tadanji dadin zaman gidan tasamu sauyi daga wajen  HANNE kishiyar mahaifiyar tata yanzu batai mata abun da take mata da ba duk dade bawani sakar mata fuska tayi ba amma ita hakanma yayi mata dadi bayan sun dawo ne da yan watanni ita ma Nadeeya tafara zuwa makaranta lokacin tana da shekara biyar shikuma yana da shekara 15 tare suke zuwa da sameer su dawo kullum shi yake daukanta yakaita har makaranta ahannun shi dake makarantar basu da ma nisa da gidan kansu kara haduwa yake suna kara shakuwa da junansu ahaka har yakammala secondary dinshi itakuma lokacin tagama primary zatashiga secondary duk dayagama tashi hakan besa yadena kaitaba kafin yasmu yashiga jami’a saboda mlm bashida isassan kudin daze sakashi university dole sai yajira wata shekarar ahaka suka cigaba da rayuwa har Allah yasa yafara zuwa university bayan shekara 2 can nagano ta a tsugunne gaban kurfoti  tana tafaman hada garwashin yaki kamawa.

ta tashi tana gunguni ta mike tsaye doguwa ce me dan jiki irin matan  nanne manya ga tsaho ga jiki kuma fara ce dan har tafi mamanta haske tana tafiya ta shiga cikin falon tana cewa ummi dan Allah kizo kiga wutannan taki kamawa tun dazu taqarasa fadar maganar da nuna gajiyawa atattare da ita tana qoqarin zama ummin tata tace wlh nadeeya kifita daga idon in rufe bana son wannan banzan sakarcin naki keda komai na mata baki iyaba duk abun da akasaki sai kice ke kaza ke wannan ke wancan to daga yanzu ma komai nagidan nan ke zanbarwa nadena taba ko tsinke tunda abun naki kullum dada gaba yake tashi daga nan kiban guri  kafin intashi kanki tashitayi dasauri tana turo baki tana qoqarin fita sukayi karo da sameer ya shigo dauke da murmushi akan fuskar shi yace to raka mata ni da nake namijima gashinan ai na hada kuma takama saki je ki dora abun daza ki dora tace yauwa yayana nakaina shiyasa nake sonka nagode ummi tace daman mana kyace haka tunda daman ai duk wani abu shiyake daure miki gindi kike yinshi zanyi maganin ku ne gaba daya sai muga inkinyi aure maga wanda ze na miki aikin gidan da ba kya kauna da sauri tace ummi ni ai ba auran da zanyi gwara inzauna awajenku nafi jin dadi tace to tunda agarin gaba gaba muke meze hana muzaun muzuba miki ido tace Allah ummi dagaske nake tace kinga fita kiban waje kije kiyi abun da nasaki tace to tafiya tana qara hade fuska ita ta tsani taji ance mata zatayi aure shikenan kuma sai ta tafi tabarsu ita bazata iyaba.

tana fita sameer ya juya ze bita ummi tai saurin kiranshi tace dawo kazauna daman ai duk kai kake qara lalatata takewa mutane abun dataga dama yarinya sai rashin son aiki ga shegiyar tsiwa yace kai ummi yanzu meye laifina danna kula da kaunwata itakadaice fa dani dole innu na mata so da kulawa tace ai sai kai tayi kaga nan gaba saika dena zuwa ko ina kazauna karinga yi mata duk abun datakeso da ayyukan ta dan bazan cigaba da wahalaba bayan ina da budurwa acikin gidana yace ai wannan me sauqi ne kar tadamu ze ringayi wlh cike da takaicin shi da yake bata shi kwata kwata komai za ace baze taba goyan bayan waniba sai de yagoyi banyanta tace kaga tashi kabar gurin nan kaida kullin baka canza hali yace Allah huci zuciyarki ummina Allah yabar mana ke yabaki tsawon kwana me amfani daman haka yake kullum idan yaga tana qoqarin jin haushi haka ze zauna yai tai mata dadin baki yana yikuwa zatasaki ranta tana jin dadin hakan har cikin ranta


bayan wasu dan shekaru ya kammala degree dinsa inda yakaranci ai likitanci fannin kwakwalwa bayan kammalawar sane kuma besamu aikin yiba sai malam ya dorashi akan harkar kasuwa inda yanema mishi tsaron wani shagon amininshi da suke kasuwancin su tare yafara zuwa cikin ikon Allah kuma sai suka samu budi adan qanqanin loakaci kuma duk da yawan ‘yan matan dasuke kawo mishi qoqon bararsu garashi tunda ga kan yan makarantarsu zuwa masu siyayya wajensa amma beta ba jin ko da wasa wata ta mishiba kwatakwata bawacce ta kwanta mishi arai haryanzu itama kuma nadeeya haryau bata kula Samari anmata fadan amma abanza taqi ji malam da yaga abun masu ba me karewa bane kawai sai yasa mu ummi da maganar akan yakamata fa suyi wani tunanin abun da yadace akan yaran nan bawai subarsu haka suna kallonsuba karkada kai ummi tayi sannan tace ni aganina malam yaran kawai muhadasu aure inaganin hakan se yafi ai yace nima nayi tuna nin hakan amma kuma da na hanga sainaga to shi sameer yaza midashi tundade be san bamu muka haifeshi ba tace hakane malam ai daman ko badade ko bajima dole mu sanar dashi gaskiyar al amari kaga kuma yanzu ai yariga da ya mallaki hankalinshi ze fahimcemu ina ganin kawai yanzu ne lokacin da yakamata musanar dashi sannan muhada aurensu nasan bazeqi hakan ba duba da yanda suka shaku da juna inaganin baze bijirewa maganar mu ba kokwa yakagani yace maganarki gaskiya ce hakan yakamata muyi kawai ai da zafi zafi akan bugi qarfe kawai je ki kirasu dukan su yanzu ayita taqare asan inda aka dosa tace to tare da mikewa taji takirasu sukazo gabadayansu suka zauna aqasa tare da cewa baba barkanka da hutawa yace barkankude saida kowa yanutsu sannan malam yafara salatin annabi sannnan yafara magana a nutse yara kiran sunan shi yace sameer zan fara dakai domin wannan kiranma gaba daya domin kane cike da ladabi da biyayya.

yace to baba yana qara sake zama da nutsuwa domin jin bayanin da akace domin sane sannan malam yace gaba dacewa  dafarko de zanfara maka nasiha akan duk abun da yasameka kadauke shi amatsayin qaddar da kuma jarabtar da Allah yayi maka domin ganin zakai hakuri da tawakkali ko kuma akasin haka ka rungumi qaddararka da hannu bibbiyu kayi addu’ar Allah ya sassauta maka ita kuma muma ka fahimce mu bada son ranmu haka ta faru ba  kajini ya amsa dacew eh baba in sha Allahu duk da yadan shiga rudin jin wadannan magan ganun da besan inda suka dosaba mlm ya dan jinjina kai yace to masha Allah haka nake sonji ina qara baka hakuri akan abun da zakaji daga garemu shide haryanzu a qagare yake dajin abun daza ace mishi saida malam yadan numfasa sannan yace gaskiyar magana malam sameer bamune iyayankaba kuma bamune muka haifeka ba hasalima bamusan inda naka iyayen suke ba kawaide a….ba qarasa maganar dayakeba mikewar da yaga sameer din yayi bashi kadai bama har nadeeya saida ta mike dan bakaramin razana sukai ba dajin wannan batun dasauri malam yakamoshi yazaunar yace dan Allah ka kwantar da hankalinka kasaurare mu ko mubakadauke mu amatsayin iyayeba mu mun daukeka amatsayin da agaremu yanzuma muna da daliline shiyasa muka gaya maka da sauri sameer yashiga girgi kai cikin shashshekar kuka da yagama wanke mishi fuska yace baba dan Allah kace min mafarki nake kar kace da gaske ne abun da kakecemin ni wlh koma ina da wasu iyaye bazan taba zuwa wajensu ba ni kune iyayena ku nasani kuma ba inda zani inatare daku rungumeshi mlam yayi yace sameer ya isa haka dan Allah be kamata karinga irin wadannan maganganun ba katsaya ka saurareni da kyau kaji kai yadaga mishi kamar wani karamin yaro yazame jikinshi da ga nashi yazaun aqasa kamar mutum mutumi haka yake agun cikin nutsuwa malam ya labarta mishi abun da yafaru abaya da yanda akai yasameshi sosai sameer yashiga tausayin kansa dashi da mahaifirya tasa ahankali yafurta Allah yasa tana raye suka amsa mishi da Ameen sannan yace baba to a ina mutumin yake yace wlh sameer bansani ba gagan gancin da nayi kenan wlh na rashin karbar number sa danayi sanna yace sade mita addu’a duk ina da take Allah yabayyana mana ita duka suka amsa da ameen malam yamaida dubansa ga Nadeeya yace ke baza ki zauna bane kinyi mana tsaye akai kamar wata yar sanda ahankali takoma ta zauna inda ta tashi   sannan yaci gaba da cewa sai abu na biyu kuma danake so na sanar da ku shine zamu hadaku aure tunda har yanzu banji wanda yace ga wanda yake so ya aura ba dan haka muka yanke hukunci da mahaifiyar ku kawai ahada ku tare tunda daman kun saba Kunsan junanku kunga kawai sai ayi tuwona maina ko yakuka gani inda me magana yayi dan ba wanda zamuyiwa dole acikin ku kunji.

sameer yace baba ai duk yanda kukayi daidene ni bani da zabin da yawuce naku saidema godiya dazan muka akan abubuwan da kuka min da dawainiya dani da bani kulawa ai ba abun da zan iyasaka muku dashi sai addu’a Allah yabiku da gidan aljannar fiddausi yabaku abun da kuke nema duniya da lahira Allah kuma ya..da sauri malam yakatseshi da cewa ya isa haka munyi maka ne domin Allah dan haka kadena ma na gdy kuma kacigaba da kallon mu matsayin iyayenka ko da wasa bamaso muga ka canza daga abun dakakeyi kajini yace In sha Allahu bazaku taba ganin wani canji da gareni ba aure kuma Allah yabamu zaman lfy malam ya amsa da ameen sannan yakalli nadeeya da ta sunkuyar da kai tunda taji anyi maganar hadasu aure yace to kefa muji ta bakinki ko kina da magana da sauri ta giragiza kai alamun bata da magana yace to naji dadi da biyayyarku agaremu kuma Allah yabaku masu yi muku kamar yanda kukayi mana suka amsa da ameen sannan yakara dayi musu nasiha sosai kuma me ratsa jiki itama ummi ta dora da tata suna gama yimusu  yace musu zasu iya tafiya ya sallamesu sukai musu godiya da sllama suka fita kowannen su jiki babu kwari…….
               
                   *
        Sai munhadu anagab kuma wannan shafin bazan mata da shiba dan har kusan kuka yasani sai da nagama typing  dinshi tsaf posting yarage min kawai arashin sani bayi saving dinshi yagoge gaba daya😭naji ciwon abun sosai wlh gashi kuma ni nayiwa kaina da kaina bare inhuce akan wani hmmm abunde ba dadi wlh

daga sabuwar marubuciyarku🖋
                ❤xeemat….love❤

Plss comment and share this book

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

AdBlock Detected

turn off ad blocker to access this site