Labarai

Na kasheta saboda tasa na Fadi Jarabawa Dalibin daya kashe Malamarsa

Da yawa daga cikin 'yan uwanta sunyi kokarin daukar mataki a hannunsu amma hakan beyu ba

An daure wani matashi a gidan yari na tsahon rayuwarsa bayan ya lakada wa malamarsa duka da sanda har saida ta rasu.

ya amsa laifinsa cikin sauki inda yake cewa “ta tsaneni a makarantar nan saboda ni kadai takewa haka domin ta dade tana cutata ina hakuri kuma wannan itace jarabawata ta karshe a wannan makarantar.

ina sa ran zan samu aiki idan sakamako na yafito saboda mahaifina ya rasu, ni nake kula da mahaifiyata da sauran kannena amma gashi ta lalata mun komai.

yakara da cewa “inajin bacin rai matuka game da zaluncin da malamar take mun, hakan yasa nakasa jurewa a wannan lokacin, bansan sanda na fusata ba na dakko wani katako da wata kujera ta karye na fara dukanta har saida naga ta daina motsi.

Yayin da yake magana da ‘yan sanda, ya bayyana damuwarsa sosai game da yadda malamar take nuna masa, kuma ya samu shedu dayawa daga cikin daliban makarantar. hakan yasa alkalin yayi mishi hukunci me sassauci.

Da yawa daga cikin ‘yan uwanta sunyi kokarin daukar mataki a hannunsu amma hakan beyu ba sedai kungiyar malamai ta makarantar sun sanar da kotu cewa a mishi duk hukuncin daya dace dashi.

daga karshe alkali ya yanke mishi hukuncin zama a gidan yari na tsahon rayuwarsa a maimakon hukuncin kisa.

ku cigaba da bibiyar mu don kawo muku labarai da duminsu.

MUN GODE – eliteBBC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

AdBlock Detected

turn off ad blocker to access this site