Labarai

Davido yana Shan Tsinuwa a wajan Musulmai saboda yayi Wasa da Sallah a Bidiyon wakar shi

An wayi gari Davido yasaki wata sabuwar wakar shi wadda akaga mutane suna sallah kuma suna rawa awajan sallar sannan kuma suka hau kan masallaci suna waka suna rawa wanda hakan ya janyo surutu a shafukan sada zumunta (social media).

kowa yasan davido ba musulmi bane sannan ya dade yana nuna alamu na kin addinin musulunci, amma wannan karan ya fito karara ya nunawa duniya cewa shi makiyin addinin musulunci ne domin yayi abubuwa dayawa a cikin bidiyon wanda basu kamata ba.

kasancewar mutane suna ta cece kuce akan wannan pepen bidiyo dayake ta yawo, hakan ya dagawa Davido hankali har yayi sanadiyar cire bidiyon nashi a kafafen sada zumunta kamar YOUTUBE, INSTAGRAM, FACEBOOK, TWITTER da sauransu.

Yada wannan bidiyo shi kanshi lefi ne shiyasa muka kawo muku kadan daga cikin wannan bidiyo inda zaku kalla a kasa.

da yawan mutane suna yiwa mawaka makauniyar soyayya amma muna fatan zaku fito ku nuna kishinku akan addinin ku sannan kuyi Allah wadai da wannan abu daya faru don yanzu haka musulmai dayawa sunyi unfollowing dinshi a shafukansa na social media sannan sunyi reporting account dinshi domin da hakane kawai za a iya dakatar da irin wadannan izgilancin da ake yiwa musulmai a fadin duniya da makamantansu.

muna fatan Allah ya shiryesu in masu shiryiwa ne kuma Allah ya hukuntasu dedai da abun da sukeyi sannan Allah ya kare musulunci da musulmai a duniya baki daya.

Allah yaji kan musulman mu da ake ta kashewa a wasu kasashen basu jiba basu gani ba.

ku kalli kadan daga cikin wannan bidiyo kuma ku cigaba da bibiyar mu domin kawo muku labarai da duminsu.

Mungode – eliteBBC

kalli bidiyo
kalli bidiyo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

AdBlock Detected

turn off ad blocker to access this site