News

ASUU SUN JANYE YAJIN AIKI

gwamnati ta tanadi billion N470 domin gyara jami'o'i da karin albashi

 

Bayan wata takwas da asuu suka shafe wajen yajin aikin, yau Allah yayi sun janye, Dalili kuwa shi ne, babbar kotun ƙoli da ake ɗaukaka ƙara ce tai umarni ga malaman jami’o’in da su koma bakin aikinsu kafin a cigaba da sauraron shari’arsu, Sannan ko wacce jami’a zasu faɗi ranar da zasu koma nan bada jimawa ba, ƙungiyar ta janye yajin aikin ne bayan ganawa da Shugabanninta a daren alhamis har zuwa juma’a, bayan sa’o’in da sukai suna tattaunawa daka ƙarshe suka yanke ƙudirinsu na komawa amma akan sharaɗi, sharaɗin kuwa shi ne se gwamnati ta basu kuɗin da suka buƙata na gyaran jami’o’i da kuma ƙarin albashi, daga ƙarshe dai gwamnati tayi amanna da wannan sharaɗin nasu

 

Gwamnatin najeriya ta tanadi naira billiyan ɗari huɗu da saba’in (₦470bn) domin gyara jami’o’i da kuma ƙarin albashin malamai, gwamnatin tace za ayi ƙarin albashin da naira biliyan ɗari da saba’in (₦170bn) sannan ayi gyaran jami’o’in da naira biliyan ɗari uku (₦300bn) Wannan shi ne tanadi na mussamman da gwamnati taiwa malaman asuu inji ministar kuɗin Najeriya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button