News

LILIN BABA YA SAKI UMMIRAHAB

shin dagaske ne lilin baba ya saki jaruma ummirahab?

A ɗan tsukunnan labarai suna ta yawo da daama akan cewa lilin baba ya saki matarsa me suna ummi rahab, kan cewar kyaunta a fuskane kawai amman bata gamsar dashi shiyasa ya saketa, wanda ake ta ƙoƙarin gano gaskiyar lamarin, kuma abin da ze tabbatarwa da mutan cewar zancen gaskiya ne shi ne, shuru da akaji jarumin yayi batare da yace komai a kan lamarin ba, a taƙaice dai daga ƙarshe jarumin ya fito ya fayyace zare da abawa, a inda yai magana a shafinsa na twitter kan cewar shi dai bai saki matarsa ba kuma ba abinda zaisa ya saketa dan yana matuƙar santa, kawai maƙiyane suke so su kashe musu aure kuma in sha Allahu shi da matarsa mutu ka raba takalmin kaza sedai maƙiya suji kunya, ashe tsabar baƙin cikin zancen da yaji ne ya hana shi magana daga ƙarshe kuma da yaji abun yana neman wuce gona da iri ya fito ya magantu, itama jarumar ta fito tayi magana akan cewar ita mijinta bai saketa ba kuma tana sonshi ba abinda zai sa su rabu maƙiya sedai suci kansu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button